Abstract

Ana samun sauye-sauye a harshe ta hanyar bunƙasa da faɗaɗa da kuma samun sababbin al’amurra cikinsa da sukan faru lokaci-lokaci. Harshe yana bunƙasa ne sakamakon ƙaruwar yawan masu magana da shi. Haka kuma yana samun naƙasu sakamakon raguwar ‘yan asalin harshen da ke magana da shi. Wannan maƙala mai taken ‘Nazarin ƙirƙira da ma’anar wasu sunayen ‘yan ta’adda a Arewa Maso Yammacin Nijeriya.’ Wannan maƙala ce da ta yi nazarin bunƙasar harshen Hausa da aka samu dalilin ayyukan masu ta’addanci a wasu yankunan Arewa maso Yammacin Nijeriya. Maƙalar ta yi ƙoƙarin fitowa da wasu sababbin sunayen da ‘yan ta’adda suke kiran kansu da su waɗanda suka ƙirƙirawa kansu domin amfani da su wajen sadarwarsu ta yau da kullum da kuma wasu sunaye da mutane suke kiran su da su. Manufar maƙalar ita ce, tabbatar da bunƙasar da harshen Hausa ya samu a dalilin ayyukan ‘yan ta’adda ta hanyar samar da ƙirƙirarrun sunaye na gama-gari da ake kiran su da su da kuma sunayen da suke laƙabawa kansu da kuma sunayen da ake yi masu. An yi amfani da ra’in ‘Dangantakar Harshe da Rikici’ (Language of Violence) na Smith, Alison G. da wasu (2008), wajen gudanar da wannan bincike wanda yake magana a kan sadarwa tsakanin ‘yan ta’adda da waɗanda ke yaƙar su. Ra’in ya bayyana cewa, idan aka yi la’akari da kalmomin da ɓangaroirin biyu ke furtawa, to akwai abubuwan da ake samarwa dangane da harshe da bunƙasarsa. Daga cikin dabarun da aka yi amfani da su wajen tattara bayanan da aka rubuta wannan maƙalar akwai; tattaunawa da ‘yan ta’adda da suka tuba da mutanen da aka yi garkuwa da su domin neman kuɗin fansa, amma daga baya suka samu ‘yanci, da ‘yan jarida da wasu ɗaiɗaikun mutane da ayyukan ta’addanci suke aukawa a cikin yankunansu. Haka kuma da sunayen da ake ji na ‘yan ta’adda a kafafen sadarwa da kuma hanyar sadarwa na rediyo da talabijin da jaridu da mujallu ta intanet.

Full Text
Published version (Free)

Talk to us

Join us for a 30 min session where you can share your feedback and ask us any queries you have

Schedule a call