Abstract

Magani musamman na Gargajiya a wajeen Bahaushe na da matuƙar matsayi da muhimmanci ga rayuwar al’ummar ƙasar Hausa, an san Bahaushe mutum ne mai matuƙar riƙo da al’adunsa wanda ya gada tun iyaye da kakanni, barantana kan abin da ya shafi harkar magani. Maƙasudin wannan nazari shi ne fito da Magungunan ciwon daji da Hausawa suke amfani da su don kawo sauƙi da waraka a rayuwar su ta yau da kullum, sani ko fahimtar magani ya na taimakawa wajen shawo kan ciwo ko cuta da wuri kafin ta azzara a jikin majinyaci, nazarin zai yi bayani kan wasu Magungunan ciwon daji. Manufar wannan bincike kuwa shi ne ƙoƙarin fito ko tantance Magungunan Ciwon daji da Hausawa suke amfani da su don warkarwa, waɗannan magunguna ga su nan a fili ko sarari don a ƙara sanin su, ba don komi ba sai don ƙara inganta rayuwa da lafiyar Hausawa ko majinyata, musamman masu fama da ire-iren Ciwon ko cututtukan daji da suke addabar al’umma. An yi amfani ta hanyar hira, wato tattaunawa da masana magunguna da masu bayar da magani da sauran mutane a wasu ɓangarorin ƙasar Hausa da kewayanta don fito da waɗannan Magungunan ciwon daji.

Full Text
Published version (Free)

Talk to us

Join us for a 30 min session where you can share your feedback and ask us any queries you have

Schedule a call